30 Disamba 2020 - 16:48
Gwamnatin Kasar Zimbabwe Ta Fara Dauke Mutane Daga Yankunan Da Ake Tsammanin Isar Mahaukaciyar Guguwa

A jiya Talata ne aka fara dauke daruruwan iyalai daga yankin Chimanimani dake gabashin kasar, gabanin isar mahaukaciyar guguwa ta Chaleni, kamar yadda ma’aikatar watsa labarai ta kasar ta sanar.

ABNA24 : Sakataren ma’aikatar watsa labarun Nick Mangwana ne ya sanar da cewa; “gwamnati tana daukar mutanen na yankin Chimanimani ne zuwa yankuna masu aminci saboda kaucewa barnar da mahaukaciyar guguwar za ta iya haddasawa.”

A halin da ake ciki dai guguwar wacce aka bai wa sunan; Chalane, tana kadawa a cikin kasar Mozambique, za kuma ta iya rikidewa zuwa mahaukaciya tare da ruwan sama mai karfi a cikin kasar baki daya, musamman a yankunan gabashin kasar dake kan iyaka.

Da akwai cibiyoyi 20 da gwamnatin kasar ta samar a cikin gundumar Manicaland.

A shekarar da ta gabata mai dubban mutane ne su ka rasa rayukansu sanadiyyar mahaukaciyar guguwar Idai,a kasar da har yanzu wasu daga cikinsu suna rayuwa a cikin hemomi.

342/